logo

HAUSA

An kaddamar da cibiyar nazarin riga-kafi ta kasashen BRICS

2022-03-23 10:40:46 CMG Hausa

Jiya Talata an kaddamar da cibiyar nazarin riga-kafi da bunkasa ci gaba wato R&D a takaice, ta mambobin kasashen BRICS, wanda aka gudanar ta kafar intanet.

A yayin bikin kaddamarwar, ministan kimiyya da fasaha na kasar, Wang Zhigang, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta yi aiki da sauran mambobin kasashen BRICS, don yin amfani da cibiyar a matsayin wata dama ta daga matsayin musaya, da hadin gwiwa wajen yin nazari, da ci gaba, da kuma gwajin riga-kafin.

Wang ya ce, Sin za ta yi aiki da wadannan kasashe domin hadin gwiwa don kafa cibiyar, da kuma lura da ingacinta, don tabbatar da karfafa ayyukan yaki da annobar COVID-19.

A yayin bikin, mambobin kasashen 5 na BRICS, sun gabatar da shawara tare, don karfafa hadin gwiwarsu a fannin samar da riga-kafin, domin tabbatar da samun damar mallakar riga-kafin, da wadatarsu, da kuma saukin farashinsu, ga kasashe masu tasowa ta hanyar tsarin raba daidai na riga-kagin a matsayin wasu kayayyakin alummun kasa da kasa.

Jamiai da wakilai daga kasashe biyar na BRICS sun halarci bikin ta kafar intanet. (Ahmad)