logo

HAUSA

Nasarorin Sin A Gida Na Da Tasirin Bunkasa Hadin Gwiwar Ta Da Kasashen Afirka

2022-03-23 20:30:29 CMG Hausa

Mai fashin baki kan harkokin siyasa da tattalin arziki, dan kasar Congo (Brazzaville) Alphonse Ndongo, ya ce irin nasarorin da kasar Sin ke samu a cikin gida, za su ci gaba da ingiza moriyar da ake samu, daga hadin gwiwar ta da kasashen Afirka.

Ndongo ya bayyana hakan ne a kwanan baya, yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua. Yana mai cewa, albarkacin kasar Sin, da yawa daga kasashen Afirka sun bunkasa, kuma Sin da kasashen nahiyar na ci gaba da morar juna cikin gwamman shekaru.

Masanin ya ce, Afirka ta ci gajiya mai tarin yawa, albarkacin hadin gwiwar ta da kasar Sin, musamman ma a fannonin raya ababen more rayuwa, da cinikayya da ayyukan gona.   (Saminu)