logo

HAUSA

Kasar Sin na son daukaka hadin kai, abota, hadin gwiwa da kasashen musulmi zuwa wani sabon matsayi

2022-03-23 10:53:34 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya bayyana a jiya Talata cewa, kasarsa a shirye take ta daukaka hadin kai, da abokantaka da hadin gwiwa da kasashen musulmi zuwa wani sabon matsayi.

Wang Yi ya bayyana hakan ne, a lokacin da yake ganawa da babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Hissein Brahim Taha a birnin Islamabad na kasar Pakistan yayin da ya halarci zaman majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar ta OIC karo na 48.

Wang ya ce kungiyar OIC dake wakiltar hadin kai da ’yancin kasashen musulmi, ta zama wata gada ta raya dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen musulmi.

Jami’in na kasar Sin ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan kiyaye 'yancin kai, da cikakkun yankunan kasashen musulmi, tare da nazarin hanyar samun ci gaba mai dacewa da yanayin kasashen. Haka kuma, kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka tare da dukkan kasashen musulmi.

Ya ce, kasar Sin za ta ba da karin alluran rigakafin COVID-19 miliyan 300 ga kasashen musulmi, tare da tallafawa kasashe mambobin kungiyar OIC a Afirka wajen yakar annobar.

Wang ya kara da cewa, kasar Sin za ta inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannin ilimi da horaswa, tare da shirya taron karawa juna sani karo na biyar game da shawarwarin wayewar kan Sin da musulunci.

A nasa jawabin, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Hissein Brahim Taha, ya yiwa Wang Yi maraba a madadin kasashe mambobin kungiyar OIC fiye da 50. Yana mai cewa, halartar taron da Wang Yi ya yi, zai kara inganta huldar dake tsakanin bangarori biyu. (Ibrahim)