logo

HAUSA

Sin ta bukaci Amurka da ta janye takunkuman da ta kakabawa wasu jami’an ta

2022-03-22 19:44:54 CMG Hausa

 

Kasar Sin ta bukaci Amurka da ta janye takunkuman da ta kakabawa wasu jami’an ta ba tare da bata lokaci ba, ko kuma tsagin na Sin ya aiwatar da matakin ramuwar gayya.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ne ya shaidawa taron manema labarai na Talatar nan hakan, yana mai cewa, Amurka ta fake da zargin keta hakkin bil Adama, wajen aiwatar da takunkumai ba bisa ka’ida ba, kan wasu jami’an kasar Sin.

Wang ya ce, sanarwar da Amurka ta fitar game da hakan, na cike da nuna wariya da karairayin siyasa, a yunkurin shafawa Sin din kashin kaji, da murzunawa jami’an ta ba tare da wani dalili ba. Hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa, ya kuma kasance mataki na tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar ta Sin.   (Saminu)