logo

HAUSA

Zelensky: Yarjejeniyar Ukraine da Rasha za ta kasance karkashin kuri’ar jin ra’ayoyin jama’ar kasa

2022-03-22 10:53:10 CRI

Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce yarjejeniyar zaman lafiyar da kasarsa za ta cimma da Rasha, ta dogara ne kan kuri’ar jin ra’ayoyin al’ummar kasar Ukraine, kamfanin dillancin labarai na Ukrinform, mallakin gwamnatin kasar ya ba da rahoton a ranar Litinin.

Zelensky ya jaddada cewa, a shirye yake ya shiga duk wata yarjejeniyar zaman lafiya, idan har al’ummar kasar Ukraine suka nuna goyon bayansu.

A ranar 18 ga watan Maris, mashawarcin shugaban kasar Ukraine, Mykhailo Podolyak, ya bayyana cewa, tsakaita bude wuta, da batun janye dakaru, da daukar kwararan matakan tabbatar da tsaron kasa, su ne manyan bukatun Ukraine a tattaunawar zaman lafiya da Rasha.(Ahmad)