logo

HAUSA

Sin Za Ta Kara Samarwa Ukraine Tallafin Dalar Amurka Miliyan 1.6

2022-03-21 20:18:18 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce gwamnatin Sin ta shirya samarwa kasar Ukraine tallafin kudi, har kimanin dalar Amurka miliyan 1.6, a matsayin agajin jin kai.

Wang Wenbin ya ce, Sin na matukar damuwa da halin matsi da fararen hula ke fuskanta a Ukraine, sakamakon tashin hankalin dake aukuwa sanadiyyar yakin Rasha da kasar ta Ukraine.

Jami’in ya ce, babban burin sassan kasa da kasa shi ne shawo kan manyan kalubalolin jin kai. Kaza lika Sin ta gabatar da shawarwari 6, da wasu matakai na hakika, domin saukakawa al’ummun Ukraine halin matsi da suke ciki. Ta kuma samar da kaso daban daban na agajin jin kai ga kasar.

Wang ya ce, Sin za ta ci gaba da taka rawar gani a fannin rage halin matsin da fararen hula ke fuskanta a Ukraine, kuma a shirye take ta ba da karin gudummawa, ta shawo kan kalubalen jin kai da tashin hankali ke haifarwa a kasar.  (Saminu)