logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Sin ya tattauna da takwarorinsu na Algeria da Tanzania

2022-03-21 10:49:42 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya tattauna da ministan harkokin wajen kasar Algeria Ramtane Lamamra, da ministar harkokin wajen Tanzania Liberata Mulamula.

Yayin tattaunawa da Lamamra, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin, Wang ya bayyana cewa, baya ga kasashen dake nuna damuwar game da abubuwan dake wakana a shiyyoyin duniya, akwai kuma kasashe da dama kamar Sin da Algeria da suke da dadadden tarihi na girmama zaman lafiya da adalci.

Ya yi kira ga irin wadannan kasashen da su hada hannu, kana su karfafa hadin kai domin daga matsayin ayyukan inganta tafarkin demokaradiyya a bisa tsarin huldar kasa da kasa.

Lamamra ya ce, kasar Algeria ta yabawa matsayar da kasar Sin ta dauka game da rikicin Ukraine, kuma ta yi amanna cewa salon da kasar Sin ke bi, wanda ya shafi goyon bayan tabbatar da adalci a matakin kasa da kasa, da kokarin neman tabbatar da zaman lafiya, da kwanciyar hankali da tsaro, su ne hanyoyi mafi dacewa kuma masu cike da kwarin gwiwa.

A yayin tattaunawa da Mulamula ta kafar bidyo, Wang ya bayyana cewa, abokantakar kasashen Sin da Tanzania ta yi tasiri a zukatan alumma. Ya ce kasar Sin tana burin zurfafa huldarta da Tanzania zuwa matsayin hulda mafi muhimmanci kuma mai kyakkyawar makoma.

Mulamula, wacce ke ziyarar aiki a kasar Sin ta kafar bidiyo, ta bayyana cewa, kasar Tanzania a shirye take ta gina huldarta da kasar Sin zuwa wani sabon matsayi karkashin ruhin hadin gwiwar Sin da Afrika. (Ahmad)