logo

HAUSA

Ya Kamata Amurka Ta Samar Wa Al’ummar Ukraine Zaman Lafiya Maimakon Makamai

2022-03-21 21:52:00 CRI

Qin Gang, jakadan kasar Sin da ke kasar Amurka, ya musunta yadda Amurka da sauran kasashen yammacin duniya suka bata sunan kasar Sin bisa hujjar batun kasar Ukraine, yayin da yake zantawa da wakiliyar CBS a ranar 20 ga wata, inda ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta ki amincewa kan labarun bogi da ake bazawa, cewa wai kasar Sin ta samar wa kasar Rasha tallafin aikin soja.

Tun bayan barkewar rikicin Ukraine, kasar Sin na himmantuwa wajen kara azama kan yin shawarwarin zaman lafiya a tsakanin bangarori masu ruwa da tsaki, tare da gabatar da shawarwari guda 6, dangane da hana barkewar kalubalen jin kai a Ukraine. Yanzu kasar Sin ta samar wa Ukraine tallafin jin kai sau da dama, tare da samar wa mazauna wurin abinci, magani, jakunan barci, madarar jarirai da dai sauransu, a maimakon samar wa Rasha ko Ukraine makamai.

Amma meye kasar Amurka ta yi? Bayan barkewar rikicin tsakanin Rasha da Ukraine, ta yi ta hada hannu da kasashen yammacin duniya wajen sanya wa Rasha takunkumi daga dukkan fannoni, da samar wa Ukraine tallafin aikin soja, tana yunkura rura wutar rikicin. Ta kuma shirya bai wa Ukraine makaman da darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 800.

Amurka tana samar wa Ukraine makamai, da sanya wa Rasha takunkumi, yayin da kasar Sin take kokarin kara azama kan yin shawarwarin zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha, da samar da tallafin jin kai. Kowa ya ganewa idonsa, waye ke rura wuta, waye kuma ke kiyaye zaman lafiya. (Tasallah Yuan)