logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Turkiyya: Rasha da Ukraine sun samu cigaba a tattaunawar tsakaita bude wuta

2022-03-21 11:25:31 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya, Mevlut Cavusoglu, ya ce kasashen Rasha da Ukraine sun samu ci gaba game da yarjejeniyar tsakaita bude wuta, sai dai har yanzu, akwai bukatar shugabannin kasashen su cimma matsaya kan sauran muhimman batutuwa.

Cavusoglu ya fadawa jaridar Hurriyet ta kasar cewa, idan har bangarorin ba su sauka daga kan matsayar da suka dauka a halin yanzu ba, to ana iya cewa akwai kwarin gwiwa game da tsakaita bude wuta.

Ya kara da cewa, alamu sun nuna cewa, bangarorin suna daf da cimma yarjejeniya kan muhimman batutuwa, Cavusoglu ya jaddada kwarin gwiwa a yayin da ya halarci tattaunawa game da tabbatar da adalci da samun ci gaba.

A makon da ya gabata, Cavusoglu ya tattauna da takwarorinsa na kasashen Rasha da Ukraine a Moscow da Kviv bi da bi. (Ahmad)