logo

HAUSA

Sin Ta Samu Gagarumin Ci Gaba Wajen Nazarin Rigakafin COVID-19 Mai Nau’in Omicron

2022-03-20 16:31:22 CRI

Babban jami’in hukumar lafiyar kasar Sin ya sanar a jiya Asabar a taron manema labarai cewa, an cimma gagarumar nasara a aikin samar da riga-kafin annobar cutar numfashi ta COVID-19 mai nau’in Omicron.

An kammala aikin nazarin riga-kafin kafin a yi wa mutane allurar. Yanzu ana gabatar da rokin fara matakin gwaji na yi wa mutane allurar, in ji Zheng Zhongwei, jami’in hukumar lafiya ta kasar Sin.

Zheng ya kara da cewa, binciken da aka gudanar ya nuna cewa, nau’in Omicron ba zai iya bijirewa riga-kafin ba, ya ci gaba da cewa, har yanzu yin cikakken riga-kafin yana da matukar tasiri wajen rage hadarin kwantar da masu fama da cutar a asibiti, da rage tsananin cutar, da kuma hasarar rayuka a sanadiyyar nau’in cutar ta Omicron.

Jami’in ya ce, samar da riga-kafin mai kara karfin garkuwar jiki shi ma yana da inganci matuka wajen rage hadarin kamuwa da cutar COVID-19 mai nau’in Omicron.

A cewar Zheng, a halin yanzu, kasar Sin tana da riga-kafin cutar kimanin 29 wadanda suka kai matakan gwaji na yi wa mutane allurar, yayin da guda 16 suke kan mataki na uku na gwaji na yi wa mutane allurar a kasashen ketare. Ya kara da cewa, an amince da riga-kafin guda bakwai shiga kasuwanni domin amfanin gaggawa, yayin da biyu daga cikinsu suna cikin jerin allurai wadanda hukumar lafiya ta duniya WHO ta amince a yi amfani da su a ayyukan gaggawa.(Ahmad)