logo

HAUSA

UNHCR na fuskantar karancin kudaden tallafawa ‘yan gudun hijirar Habasha

2022-03-20 17:19:36 CRI

 

Ofishin babban jami’in hukumar tallafawa ‘yan gudun hijira ta MDD (UNHCR), ya sanar da cewa, ta samu kashi 13 bisa 100 kadai daga cikin dalar Amurka miliyan 205.4 da yake bukata domin gudanar da ayyukan tallafawa mutanen da suka kauracewa gidajensu da ‘yan gudun hijira a kasar Habasha.

A cikin rahoton baya-bayan nan da ta gabatar kan halin da ake ciki a arewacin Habasha, hukumar UNHCR ta ce, ta karbi dalar Amurka miliyan 25.9 daga cikin dalar Amurka miliyan 205.4 da take bukata domin tallafawa ‘yan gudun hijira 93,500 dake neman mafaka a Habasha, da kuma masu neman wurin kwana da yawansu ya kai miliyan 2.6.

A cewar UNHCR, ana bukatar kudaden ne domin samar da wuraren zama, da ba da ilmi, da kiwon lafiya, da kuma samar da ruwan sha da tsaftar muhalli, don biyan bukatun mazauna sansanonin ‘yan gudun hijirar Habasha.(Ahmad)