logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a yi bayani game da batun tsaro da ya shafi kwayoyin halittu masu hadari a Ukraine

2022-03-19 17:04:32 CRI

Zaunannen wakilin Kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki game da batun kwayoyin halittu masu hadari a Ukraine, da su yi bayani game da daftarorin da aka gano a baya-bayan nan, domin kawar da shakku daga zukatan al’ummun duniya.

Ya ce kasar Sin ta taba fama da tasirin makamai masu guba da kwayoyin halittu masu hadari. Kuma ta yi ammana cewa, ya kamata duk wani bayani game da ayyukan soji da suka shafi kwayoyin halittu masu hadari, ya ja hankalin al’ummun duniya domin kare aukuwar hadari mai muni.

Zhang Jun, ya shaidawa Kwamitin Sulhu na MDD cewa, ya kamata dukkan masu ruwa da tsaki su dauki matakin da ya dace. Ya ce Rasha ta kara bayyana wasu daftarori da ta gano a baya-bayan nan, don haka, kamata ya yi wadanda abun ya shafa, su amsa tambayoyin da ake da su, tare da yin bayani akan kari, domin kawar da shakku.

Ya ce matsayar kasar Sin kan makaman kare dangi a bayyane take, kuma ba ta sauya ba. A cewarsa, Sin na goyon bayan haramtawa da lalata dukkan makaman kare dangi, ciki har da masu guba da kwayoyin halittu masu hadari. (Fa’iza Mustapha)