logo

HAUSA

Girgizar kasa a Japan ta hallaka mutane 3 da jikkata 126

2022-03-17 10:55:48 CRI

 

Mutane 3 sun rasu kana wasu mutanen 126 sun jikkata, sakamakon wata girgizar kasa mai karfin maki 7.4, da ta auku a gundumomi 7 da suka hada da Miyagi da Fukushima, a arewa maso gabashin kasar Japan.

A cewar hukumomin ’yan sanda da na ba da agajin gaggawa dake kasar, girgizar kasar ta auku ne a daren jiya Laraba, an kuma ji motsi mai karfi a yankunan arewa maso gabas, da gabashin kasar, musamman a Miyagi da Fukushima.

Sakamakon hakan, mahukunta sun yi gargadin aukuwar ambaliyar tsunami a sassan dake bakin teku, na yankunan Miyagi da Fukushima, inda aka yi kira ga mazauna da su kauracewa bakin teku. (Saminu Hassan)