logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira ga hadin gwiwarta da EU wajen magance kaluabalen duniya

2022-03-17 11:37:53 CMG

Zaunannen jakadan kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira ga hadin gwiwar kasarsa da Tarayyar Turai wajen magance kalubalen da duniya ke fuskanta.

A cewarsa, duniya yanzu na fuskantar dimbin kalubale. kuma Sin da Tararrayar Turai na da karfin ingiza zaman lafiyar duniya, haka kuma manyan kasuwanni ne da ka iya inganta ci gaba na bai daya da kyautata rayuwar bil adama.

Zhang Jun ya bayyana yayin taron Sin da Tarayyar Turai kan harkokin mata da mabanbantan halittu cewa, Sin da EU din na da alhaki da kuma ikon karfafa hadin gwiwa a duniya.

Ya kara da cewa, a shirye Sin din take ta zurfafa hadin gwiwarta da EU da sauran mambobinta, domin daukaka ka’idoji da muradun MDD, da kare tsarin huldar kasa da kasa da ingiza MDD ta kara taka rawa wajen shawo kan kalubalen duniya. (Fa’iza Mustapha)