logo

HAUSA

Hauhawar farashin kaya a Najeriya ya kai kashi 15.7 a watan Fabrairu

2022-03-16 20:46:07 CRI

Alkaluman da hukumar kididdiga ta Najeriya (NBS) ta fitar jiya Talata na nuna cewa, hauhawar farashin kayayyaki a kasar, ta karu zuwa kashi 15.7 cikin 100 a watan Fabrairu, daga kashi 15.6 cikin 100 da aka samu a watan Janairu

Rahoton ya kara da cewa, an samu tashin farashin kayan abinci ne, sakamakon karin farashin burodi da hatsi da kayayyakin abinci irin su dankalin Turawa, da doya, da mai girki da kuma 'ya'yan itatuwa.

Bugu da kari, an samu karuwar farashi mafi girma a fannin gas, da man fetur, da barasa, da tabar sigari, da kayan shaye-shaye,da gawayi da katako,da fannin tsafta,da gyara, da takalma, da sauran kayan kawa .