logo

HAUSA

Sin za ta mayar da martani idan Amurka ta nace ga saka mata takunkumi

2022-03-16 21:00:37 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ba da amsa kan barazanar saka takunkumi da Amurka ta yi wa kasar Sin, a yayin taron manema labarai da aka saba yi a yau Laraba, inda ya jaddada cewa, kasar Sin tana adawa da duk wani nau'i na takunkumin da Amurka ta kakaba mata, kuma idan har Amurka ta dage kan ganin bayan ta, to ko shakka babu kasar Sin za ta mayar mata da martani.

Kwanan nan, jami'an Amurka sun sha bayyana cewa, idan kasar Sin ta yi watsi da gargadin da Amurka ta yi mata game da taimakawa Rasha kan batun Ukraine, to za ta fuskanci mummunan sakamako.

Zhao Lijian ya jaddada cewa, takunkumi bai taba zama wata hanya mai dacewa ta warware matsaloli ba, kuma kasar Sin za ta ci gaba da kiyaye daidaikun hakkoki da moriyar kamfanoni da jama'arta. A yayin da take neman samun goyon baya da hadin gwiwa daga kasar Sin, a daya bangaren kuma, Amurka ta sanyawa kasar Sin takunkumi, wanda hakan ba abu da za ta lamunta ba.

Ban da wannan kuma, game da kalaman ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov kan dakin gwaje-gwajen kwayoyin halittu na soji na Amurka, Zhao Lijian ya bayyana cewa, ya kamata Amurka ta martaba yarjejeniyar haramta makaman masu guba, ta kuma yi karin haske kan damuwar da al'ummar duniya ke nunawa kan wannan batu.

Rahotanni na nuna cewa, Sergey Lavrov ya fada a baya-bayan nan cewa, Amurka na da daruruwan dakunan gwaje-gwajen kwayoyyin halittu na soja a wurare daban daban na duniya, ciki har da kusan 30 a Ukraine, wanda ke yin mummunar barazana ga dimbin fararen hula.

Zhao Lijian ya kara kalubalantar bangaren Amurka, da ya canja matsayinsa na adawa da kafa tsarin bincike, yana mai nuni da cewa, hakan zai taimaka wajen dawo da amincewar kasashen duniya kan Amurka, na sauke nauyin da suka rataya a wuyanta kan harkokin kasa da kasa, har ila yau, zai taimaka wajen karfafa matsayin kare tsaron halittun duniya. (Mai fassara: Bilkisu)