logo

HAUSA

Yara kusan miliyan 12.8 sun harbu da COVID-19 a Amurka

2022-03-16 09:48:04 CMG

Kimanin yara miliyan 12.8 ne gwajin da aka yi musu ya nuna sun kamu da cutar COVID-19 a kasar Amurka tun bayan barkewar annobar, kamar yadda rahoton baya bayan nan da kwalejin lura da asibitocin kananan yara ta kasar Amurka (AAP) ta gabatar.

Jimillar kananan yara miliyan 12,752,636 ne suka kamu da cutar COVID-19 a duk fadin kasar ta Amurka ya zuwa ranar 10 ga watan Maris, kuma adadin yaran ya kai kashi 19 bisa 100 na dukkan mutanen da suka kamu da annobar, a cewar rahoton.

Rahoton ya kara da cewa, an samu karin sabbin adadin yara 411,000 da suka kamu da cutar cikin makonni hudu da suka gabata. Sannan kusan yara 42,000 suka kamu da cutar COVID-19 a kasar a makon jiya. (Ahmad)