logo

HAUSA

Kasar Sin ta kuduri aniyar sa kaimi don ganin an hanzarta daidaita halin da ake ciki tsakanin Rasha da Ukraine

2022-03-15 21:11:59 cri

A ranar 14 ga wata bisa agogon wurin, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana daraktan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin tsakiya na kasar Yang Jiechi, ya yi ganawa da Jake Sullivan, mai baiwa shugaban kasar Amurka shawara kan harkokin tsaro, a birnin Rome na kasar Italiya. Bayanai na cewa, Sullivan ya nuna damuwa game da goyon bayan da kasar Sin ke baiwa kasar Rasha yayin ganawar.

Game da haka, a yayin taron manema labaru da aka saba yi a yau Talata, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya jaddada cewa, kan batun halin da ake ciki a kasar Ukraine, kasar Sin ta kuduri aniyar inganta zaman lafiya da yin shawarwari, da hanzarta sassauta yanayi, da nuna adawa da kokarin da Amurka ke yi na neman jirkita gaskiya da bata sunan kasar Sin.

Baya ga haka, game da bayanan karyar da Amurka ta yi cewa, wai kasar Sin tana da niyyar tallafawa Rasha a fannonin aikin soja da tattalin arziki, Zhao Lijian ya mayar da martani cewa, sakataren shugaban kasar Rasha kan yada labarai Dmitry Peskov ya riga ya musanta wannan batu a ranar 14 ga wata, kasar Amurka ta kan kirkira tare da yada bayanan karya, wannan mataki ne na rashin kwarewa da da'a da sanin ya kamata. (Mai fassara: Bilkisu)