logo

HAUSA

Tsakanin watannin Janairu da Fabarairu adadin jarin waje da Sin ta yi amfani da shi ya karu da kaso 37.9 bisa dari

2022-03-15 11:15:18 CRI

Wasu alkaluma da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar, sun nuna yadda jarin waje da kasar Sin ta yi amfani da shi tsakanin watannin Janairu da Fabarairun bana ya karu da kaso 37.9 bisa dari, inda adadin ya kai kudin kasar yuan biliyan 243.7.

A fannin masana’antu, jarin waje da Sin ta yi amfani da shi a bangaren ba da hidima ya kai yuan biliyan 175.7, adadin da ya karu da kaso 24 bisa dari a shekara. A bangaren masana’antun manyan fasahohi ma, adadin jarin waje da Sin ta yi amfani da shi ya karu da kaso 73.8 bisa dari a shekara, ciki har da kaso 69.2 bisa dari a fannin samar da hajoji a fannin, da kuma kaso 74.9 bisa dari a fannin samar da hidimomi a wannan bangare.

Alkaluman su bayyana cewa, shirin ziri daya da hanya daya, ta samar da kaso 27.8 bisa dari na jarin waje, da kaso 25.5 bisa dari karkashin shirye shiryen kungiyar ASEAN.

Masu fashin baki na cewa, mahukuntan kasar Sin na fatan aiwatar da wasu sabbin matakai, na daidaita jarin waje da kasar ke amfani da shi sannu a hankali, yayin da ake fatan irin wannan jari na waje zai ci gaba da bunkasa cikin watanni 4 na farkon shekarar nan. (Saminu)