logo

HAUSA

Firaministan Sin ya jaddada muhimmancin dorewar bunkasar tattalin arzikin kasa

2022-03-15 11:17:41 CRI

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada muhimmancin daukar kwararan matakai domin haye wahalhalu don tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arzikin kasa mai dorewa, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci taron tattaunawar majalisar gudanarwa ta kasa a ranar Litinin.

Taron ya gabatar da muhimman bangarorin da za a mayar da hankali a cikin rahoton ayyukan gwamnati na wannan shekara ga hukumomin da abin ya shafa na majalisar gudanarwar kasa da ta kananan hukumomi, kana ya bukaci a aiwatar da kudurorin yadda ya kamata.

Ya bayyana cewa, tattalin arziki yana fuskantar sabbin matsin lamba da karuwar kalubaloli, taron ya jaddada bukatar hada ayyukan kandagarkin annobar COVID-19 da na bunkasa cigaban tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al’umma tare, kana ya jaddada bukatar bayar da fifiko wajen tabbatar da dorewar bunkasuwar tattalin arziki zuwa matsayin koli.

Daga karshe, kasar Sin zata ci gaba da sa lura game da sauye-sauyen da ake samu a yanayin tattalin arzikin duniya, da yin sauye-sauye a manya da kananan manufofin tattalin arziki, da yanayin gudanar ayyukan kasuwannin muhimman kayayyakin bukatu, da kuma tasirin da zasu haifarwa kasar Sin.

Taron yace, za a tabbatar da dorewar samar da makamashin kwal da lantarki.

Sannan za a tabbatar da cikakken aiwatar da manufofin da zasu taimaka wajen magance wahalhalun da kamfanoni zuba jarin waje da kuma kamfanonin kasuwancin ketare ke fuskanta.(Ahmad)