logo

HAUSA

UNOCHA na kara azamar samar da tallafin jin kai ga Somalia

2022-03-15 10:35:05 CRI

Ofishin tsara ayyukan jin kai na MDD ko UNOCHA a takaice, ya ce yana kara azama wajen samar da tallafin jin kai, ga sassan al’ummun da matsalar fari ta fi shafa a kasar Somalia.

Cikin wata takardar bayani da ofishin ya fitar, ya ce matsalar fari na kara ta’azzara a Somalia, inda adadin masu fama da rashin abinci ya daga daga mutum miliyan 3.2 a watan Disambar bara zuwa miliyan 4.5 a yanzu.

OCHA ya ce domin shawo kan wannan matsala, yana tsara ayyukan sa na ba da agajin jin kai, ta hanyar gano wuraren da matsalar ta fi kamari, tare da kasa al’ummun yankunan kasar zuwa rukunoni daban daban gwargwadon bukatar neman tallafi, ta yadda za a rika ba su agaji daki daki, bisa tsari mafi dacewa da yanayin da suke ciki.   (Saminu)