logo

HAUSA

Wakilan Rasha da na Ukraine za su tattauna ta kafar bidiyo

2022-03-14 09:56:17 CRI

Nan gaba a yau Litinin ne ake sa ran wakilan kasashen Rasha da Ukraine, za su sake tattaunawa ta kafar bidiyo, yayin da bangarorin dake nazarin hanyoyin aiwatar da matakai ke ci gaba da na su ayyukan.

Da yake bayyana hakan a jiya Lahadi, kakakin fadar gwamnatin Rasha Dmitry Peskov, ya ce an dauki wannan mataki ne, saboda bukatar da ake da ita ta ci gaba da maida hankali kan muhimman batutuwa da dama.

Shi ma mashawarcin shugaban Ukraine Mykhailo Podoliak, ya wallafa a shafin sa na Tiwiwa cewa, ana sa ran tattaunawar ta yau, za ta samar da zarafin tattara sakamakon farko da aka cimma tsakanin sassan biyu.

Tun daga ranar 28 ga watan Fabarairu, wakilan kasashen biyu suka fara tattaunawa da juna kai tsaye a Belarus, inda suka gudanar da shawarwari har karo 3, ko da yake ba su kai ga cimma wani sakamako na a zo a gani ba. (Saminu)