logo

HAUSA

Shugabannin Faransa da Jamus sun sake shiga tsakani kan rikicin Rasha da Ukraine

2022-03-13 16:53:09 CRI

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz sun tattauna da shugaban Rasha Vladimir Putin, da na Ukraine Volodymyr Zelensky, daya bayan daya a jiya Asabar, don sake shiga tsakani kan rikicin kasashen Rasha da Ukraine.

A cewar shafin yanar gizo na shugaban Rasha, a yayin tattaunawar da aka yi a wannan rana, shugaba Putin na Rasha, ya bai wa Macron da Scholz cikakken bayani kan jerin shawarwarin da aka yi ta kafar bidiyo a baya-bayan nan tsakanin wakilan Rasha da na Ukraine, da kuma ainihin halin da ake ciki na jin kai a yankunan aikin soja na musamman, ya kuma lissafta hujjojin da cewa, bangaren Ukraine ya yi matukar karya dokar jin kai ta kasa da kasa, kamar jibge manyan makamai a kusa da wuraren zama, da asibitoci, da makarantu, da gidajen renon yara da sauransu.

A wannan rana kuma, fadar Elysee ta shugaban kasar Faransa, ta fadawa kafafen yada labaran kasar cewa, Faransa da Jamus sun bukaci Rasha ta kawo karshen harin da ake kai wa Mariupol na Ukraine. Baya ga haka, ta ce, Putin bai nuna ra’ayin tsagaita bude wuta ba, don haka Faransa ta yanke shawarar sanyawa Rasha sabbin takunkumai.

A nasa bangaren, Zelensky ya fada a shafukan sada zumunta cewa, ya tattauna da Scholz da Macron kan batutuwan da suka shafi makomar shawarwarin a tsakanin Ukraine da Rasha da dai makamantansu, inda ya nemi Scholz da Macron da su taimaka wajen ganin an saki magajin garin Melitopol dake yankin Zaporozhye. (Mai fassara: Bilkisu Xin)