logo

HAUSA

Patama Leeswadtrakul: Gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing ta gabatar da abubuwan gado masu daraja

2022-03-12 16:46:11 CRI

Shugabar kwamitin kula da harkokin al’adu da abubuwan gado na kwamitin shirya gasar Olympics na duniya, kana, mambar kwamitin gasar Olympics na kasa da kasa na kasar Thailand, Patama Leeswadtrakul ta yaba matuka da gasar Olympics ta lokacin hunturu da gasar Olympics ta lokacin hunturu ta nakasassu ta birnin Beijing. Tana mai cewa, kasar Sin ta nuna wa kasashen duniya kwarewarta wajen aiwatar da babbar gasa ta kasa da kasa, inda ta bar dimbin abubuwan gado masu daraja a fannin wasannin Olympics.

Ta ce, gasar Olympics ta lokacin hunturu ta nakasassu ta Beijing ta cimma nasarar sa kaimi ga masu bukata ta musamman a kasashen duniya da su fara wasannin motsa jiki. Ta ce kasar Sin tana da kwarewa matuka wajen gudanar da irin wannan babbar gasa ta duniya, ta kuma mai da hankali kan gudanar da gasar ta hanyar kare muhalli.

Bugu da kari, ta ce an daidaita wuraren wasannin motsa jiki na gasar Olympics da dama zuwa wuraren wasannin motsa jiki na gasar Olympics ta lokacin hunturu ta nakasassu, bisa bukatun ‘yan wasan motsa jiki masu bukata ta musamman, lamarin da ya nuna kulawar Sin kan masu bukata ta musamman sosai. (Maryam)