logo

HAUSA

Samun saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin na kashi 5.5% ba abu ne mai sauki ba

2022-03-11 13:49:50 CRI

Yau da safe ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana a gun taron manema labarai bayan rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar na NPC cewa, samun saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin na kashi 5.5% ba abu ne mai sauki ba.

Li Keqiang ya nuna cewa, GDPn kasar Sin a bara ya kai fiye da kudin Sin Yuan triliyan 110, karuwar a kashi 5.5% bisa babban tushe, adadin karuwar da zai kai jimillar tattalin arzikin wata kasa mai matsakaicin karfi. Saboda haka, cimma wannan buri yana da wahala sosai.

Ban da wannan kuma, Li Keqiang ya kara da cewa, matakan da Sin take dauka a bana, ba na gajere lokaci ne kawai ba, har ma bisa ga halin da ake ciki, tare da yin hangen nesa, gami da biyan bukatu masu dorewa a nan gaba. (Amina Xu)