logo

HAUSA

Wang Yang ya bukaci majalisar CPPCC ta bada gudummawar kyautata zaman rayuwar al’umma

2022-03-10 10:55:18 CRI

Shugaban majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta CPPCC Wang Yang, a yau Alhamis ya bukaci majalisar da ta yi kokarin cimma muradun al’umma na samun ingantacciyar rayuwa, kana ya bayar da gudummawar kyautata zaman rayuwar al’umma.

Wang Yang ya yi wannan tsokaci ne a wajen rufe taro na biyar na  majalisasr CPPCC karo na 13.

Ya ce ya kamata majalisar CPPCC ta sauke dukkan nauyin al’umma dake bisa wuyanta, inda ya bukaci majalisar da ta saurari muryoyin al’umma domin share musu hawaye.

Ya kara da cewa, ya kamata majalisar ta bayar da shawarwari game da hanyoyin da za a cimma muradun al’umma domin kyautata rayuwarsu da kuma taimakawa jam’iyyar kwaminis ta Sin da gwamnatin kasar wajen kyautata zaman rayuwar al’ummar kasa.

Wang Yang ya kuma yi kira da a aiwatar da matakan kyautata tuntuba da kaucewa bin dogayen sharudda.(Ahmad)