logo

HAUSA

Biden ya sanar da kakabawa Rasha takunkumin makamashi

2022-03-09 11:28:10 CRI

 


Shugaban kasar Amurka Joe Biden jiya Talata, ya sanar da kakabawa kasar Rasha takunkumin hana shigo da man fetur da iskar gas da kuma kwal cikin kasar daga kasar Rasha, sakamakon ayyukan soji da take yi a kasar Ukraine.

Shugaban ya bayyana haka ne, yayin jawabin da ya gabatar daga fadar White House. Wannan yana nufin cewa, man kasar Rasha ba zai kara samun karbuwa a tashoshin jiragen ruwa na Amurka ba. Ya kuma yi ikirarin cewa, matakin zai yi mummunar illa ga ikon da Rasha ke da shi na ci gaba da samun kudaden gudanar da ayyukanta na soji. Sai dai ya yarda cewa, matakin zai iya yin illa ga Amurkawa a cikin gida, ta hanyar haifar da hauhawar farashin man fetur a gidajen mai.

A halin da ake ciki kuma, kungiyar Tarayyar Turai(EU) da ke dogaro da kasar Rasha wajen samun kashi 40 cikin 100 na iskar gas da take samarwa, ta sanar a safiyar jiya cewa, ta bullo da wasu sauye-sauyen matakan da suka dace, da rage shigo da iskar gas daga Rasha da kashi biyu bisa uku a bana, da nufin rage dogaron da take kan Rasha a fannin makamashi nan da 2030. Amurka dai ba ta dogara da makamashin Rasha ba fiye da kasashen Turai.

Kwanan nan shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya bayyana yayin wani taro da ma'aikata mata na jiragen sama na Rasha cewa, takunkuman da kasashen yammacin duniya suka kakabawa kasar, kusan daidai yake da shelanta yaki.(Ibrahim)