logo

HAUSA

Masanin Masar: Ingancin bunkasuwar tattalin arzikin Sin ya zama abin koyi ga duniya

2022-03-09 14:59:13 CRI

 Kasa da kasa na mai da hankali kan manyan taruka biyu na NPC da CPPCC da ake gudana a nan birnin Beijing, daga cikinsu akwai masanan Masar dake sanya ido matuka kan alkaluman bunkasuwar tattalin arizkin Sin a bara da hasashen da ake yi a wannan fanni a bana.

Masani a kwalejin nazarin siyasa ta hukumar watsa labarai ta kasar Masar Hussein Ismail, yayin da ya tabo rahoton ayyukan gwamnatin Sin na bana ya nuna cewa, duk da cewa Sin na fuskantar matsin lambar da illar cutar COVID-19 ta haifar mata, amma tana samun ci gaban tattalin arziki bisa mataki mai kyau, inda aka yi hasashe cewa, karuwar GDP a cikin gida, zai karu da kimanin kashi 5.5%, abin da ya bayyana boyayyen karfi da ingancin bunkasuwar tattalin arzikin kasar.

Ya ce:

“A shekarar bana, an yi kiyasin cewa, karuwar GDPn kasar Sin zai kai kimanin kashi 5.5%, karuwar tattalin arzikin Sin na kan wani mataki mai kyau, idan an kwatanta da halin da duniya ke ciki. Ganin yadda cutar COVID-19 ke ci gaba da bazuwa a sassan duniya, tattalin arzikin duniya a bara ya fuskanci koma baya, da har ake ganin ba za a samu farafadowa yadda ya kamata ba, duk da haka Sin ita ce kasa daya tilo a duniya dake samun karuwar tattalin arziki. Muradun da aka saka cikin rahoton ayyukan gwamnatin da aka gabatar na bayyana cewa, bunkasuwar tattalin arzikin Sin na kara inganta.”(Amina Xu)