logo

HAUSA

Mata 'yan majalisun NPC da CPPCC sun bayyana ra’ayinsu game da kare hakkin mata a manyan taruka 2

2022-03-08 14:17:21 CRI

Yau Talata 8 ga wata ranar mata ce ta duniya, kuma a daidai lokacin da manyan taruka 2 (taron shekara shekara na majalisar wakilan jama’ar  kasar Sin da na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar) ke gudana a kasar Sin. A tarukan na wannan shekara, ‘yan majalisun biyu mata sun gabatar da shawarwarinsu game da kare hakkin mata da tabbatar da lafiyar mata.

Rahoton ayyukan gwamnatin kasar Sin na bana na cewa, ya kamata a zage damtse wajen dakile ayyukan fataucin mata da kananan yara, da kuma tabbatar da hakkinsu yadda ya kamata bisa doka. ‘Yar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin kana lauya Madam Peng Jing ta ce, wannan lamari ya faranta ran mutane sosai. A taron na bana, Peng Jing ta gabatar da shawararta mai taken “Kara karfin dakile faraucin mata da kananan yara bisa ka’ida mai karfi”.

Yadda za a kara karfin tabbatar da lafiyar mata shi ma yana jawo hankalin ‘yan majalisun biyu sosai. ‘Yar majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Wang Ling ta ba da shawara cewa, ya kamata a kara karfin yin gwaji kan cututukan sankara 2 wato ciwon sankara a mahaifa da ciwon sankara a mama da shigar da su cikin inshorar jiyya. Ta ce:

“Da farko a kara karfin yiwa mata da shekarunsu suka dace gwaji kyauta. Kuma ina ba da shawarar shigar da wannan aiki a cikin inshorar jiyya. Na biyu, ina ba da shawarar a kara karfin fasahar zamani a wannan fanni. Na uku kuma, ina kira ga mahukuntan kasarmu da su hanzarta samar da allurar riga kafi.”(Amina Xu)