logo

HAUSA

Jakada Cui Jianchun ya gana da ministan harkokin wajen Najeriya

2022-03-08 19:42:02 CRI

A jiya Litinin ne jakadan Sin a Najeriya Cui Jianchun, ya gana da ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama. Yayin tattaunawar da suka yi, jakada Cui ya ce kasar sa na fatan yin aiki tare da Najeriya, wajen karfafa hadin gwiwa a fannin amincewa juna ta fuskar siyasa, da kara inganta hadin kan sassan biyu, a bangaren raya tattalin arziki da cinikayya.

A nasa bangare kuwa, Mr. Onyeama cewa ya yi, Najeriya da Sin na da alakar abota ta kut da kut, da hadin gwiwa a manyan fannoni da dama, wadanda dukkanin su ke haifar da manyan nasarori. Ya ce Najeriya na da burin ci gaba da fadadawa, da zurfafa hadin gwiwar zahiri tsakanin ta da Sin, ta yadda sassan biyu, da al’ummun su za su ci gajiya daga hakan.  (Saminu)