logo

HAUSA

Wang Yi: Kasashe daban-daban na bukatar hadin kai da sulhuntawa

2022-03-07 16:22:41 CRI

 Yau Litinin, an shirya taron manema labarai game da taron shekara-shekara na majalisar wakilai na 13 na jamhuriyar jama’ar kasar Sin a babban dakin taron jama’a, inda ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya amsa tambayoyin da ’yan jaridun gida da waje suka gabatar masa.

Wang Yi ya nuna cewa, wannan shekara da muke ciki na cike da kalubaloli. Saboda hakan, kasashe daban-daban na bukatar hadin kai da sulhuntawa a maimakon kawo baraka da yin fito-na-fito. A matsayinta na kasa dake sauke nauyin dake wuyanta, Sin za ta ci gaba da nacewa ga matsayin tafiyar da harkokin duniya tsakanin kasa da kasa, don hada kan duk kasar dake da burin shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwa, ta yadda za mu kara hadin gwiwa don tinkarar kalubaloli da ci gaba da ingiza kafa kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya da samun bunkasuwar duniya baki daya mai armashi nan gaba. (Amina Xu)