logo

HAUSA

IMF: Rikicin Ukraine ya haifar da koma bayan tattalin arziki mai tsanani

2022-03-06 16:33:12 CRI

Jiya Asabar 5 ga wata, asusun ba da lamuni na duniya wato IMF, ya fitar da wata sanarwa, inda aka bayyana cewa, duk da cewa yanayin siyasa da kasar Ukraine ke ciki yana sauyawa cikin sauri, kuma makomar kasar tana cikin yanayin rashin tabbas, amma rikicin kasar ya riga ya haifar da koma bayan tattalin arziki mai tsanani, don haka asusun IMF zai ci gaba da gudanar da bincike kan yanayin da kasar ke ciki, kuma zai samar da shawarwarin manufofi da tallafin kudi da taimakon fasahohi ga kasashe mambobin asusun bisa bukatunsu.

Sanarwar ta bayyana cewa, karuwar farashin hajojin da suka hada da makamashi, da alkama, ya kara tsananin karyewar darajar kudi, sakamakon farfadowar tattalin arziki bayan barkewar yaduwar annobar COVID-19, musammam ma ga iyalai dake fama da talauci a fadin duniya.

Sanarwar ta kara da cewa, rikicin Ukraine ya riga ya haifarwa tattalin arzikin kasashen duniya da dama mummunan tasiri, shi ya sa ya dace a dauki matakin da ya dace domin dakile matsalar. (Jamila)