logo

HAUSA

Sin na adawa da ware yankin Taiwan daga kasar da tsoma baki cikin batun yankin daga wasu kasashen waje

2022-03-05 11:33:03 CRI

Game da batun yankin Taiwan, cikin rahoton gwamnatin kasar Sin, an bayyana adawa da raba yankin Taiwan daga kasar Sin, bisa yadda wasu kasashen waje ke tsoma baki cikin batun yankin.

Rahoton ya bayyana cewa, ya kamata a bi manufofin da aka tsara kan batun yankin Taiwan, da daidaita batun bisa ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya, da ra’ayin da aka cimma daidaito kan sa, don gane da batun yankin Taiwan a shekarar 1992, domin ta haka ne za a iya sa kaimi ga dinkewar dukkanin kasar Sin, da zaman lafiya a gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan yadda ya kamata.

Rahoton ya kara da cewa, ya kamata jama’ar gabobin biyu, su yi kokarin raya al’ummar kasar Sin tare. (Zainab)