logo

HAUSA

Rasha da Ukraine na shirin gudanar da zaman tattaunawa karo na 3

2022-03-05 12:13:34 CRI

 

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya ce kasarsa na fatan ci gaba da tattaunawa da bangaren Ukraine, tana kuma da burin wanzar da zaman lafiya, muddin aka amince da bukatun tsaro da Rasha ke muradi.

A nasa bangare, mashawarci ga shugaban kasar Ukraine Mykhailo Podolyak, ya ce mai yiwuwa sassan biyu su gudanar da zagaye na 3, na tattauna a Asabar din nan ko gobe Lahadi. Sai dai kuma Mr. Podolyak ya ce sassan biyu suna da wasu bukatu masu wuya, wanda hakan ke zama kadangaren bakin tulu, ga burin da ake da shi na cimma matsaya.

A daya bangaren kuma, mahukuntan Ukraine, sun ce dakarun kasar Rasha sun amshe iko da tashar nukiliya ta Zaporizhzhia, wadda ita ce irin ta mafi girma a daukacin nahiyar Turai, kuma daga bisani kakakin ma’aikatar tsaron kasar Rasha Igor Konashenkov ya tabbatar da hakan.

Da yake tsokaci game da halin da ake ciki, wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira ga sassan da batun ya shafa, da su yi aiki tare, da tallafin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, wajen tabbatar da kare kayayyakin na’urorin makamashin nukiliya dake cikin Ukraine.   (Saminu)