logo

HAUSA

An zargi hukumar shigi da ficin Amurka da gaza kare mutanen da ake tsare da su daga cutar COVID-19

2022-03-04 10:57:42 CRI

Cutar COVID-19 tana ci gaba da yaduwa cikin sauri a cibiyoyin tsare mutane da jami’an hukumar shigi da fici ta Amurka ICE ke lura da su, inda ake barazana ga rayukan mutanen da ake tsare da su a duk fadin kasar, kamar yadda wani lauyan kungiya mai zaman kanta ta American Civil Liberties Union (ACLU) ya bayyana.

A sanarwar da babban lauyan kungiyar ACLU, Eunice Cho, ya fitar, ya ce, kimanin watanni da dama ke nan aka bukaci jam’an hukumar ta ICE da su bayar da damar yiwa mutanen da ake tsare da su riga-kafi mai kara karfin garkuwar jiki, amma sun gaza yin hakan.

Cho, ya yi zargin gazawar hukumar ICE na samar da kariyar da cewa abin takaici ne kuma ya saba dokokin tsarin mulkin kasa.

Ya ce kungiyar ACLU, da kuma ofishinta dake Washington D.C. sun shigar da kara a ranar Talata, a madadin mutanen da aka tauye musu hakkin kula da lafiyar wadanda ake tsare da su a hannun hukumar ICE, sun bukaci a ba su riga-kafin COVID-19 mai kara garkuwar jikin amma an hana su.

Mai shigar da karar ya bukaci mutanen da yake karewa, wadanda ke cikin yanayi mai tsanani na fama da tabarbarewar lafiya har ma da barazanar mutuwa a sakamakon fama da cutuka, da kuma mutanen da aka tauye musu hakki na rashin ba su damar karbar riga-kafin mai kara garkuwar jiki dake tsare a hannun jami’an hukumar ICE. (Ahmad)