logo

HAUSA

Rasha da Ukraine sun kammala zagaye na biyu na tattaunawa inda suka amince da samar da hanyoyin kai agajin jin kai

2022-03-04 10:13:08 CRI

Yayin zagaye na biyu na tattaunawarsu a Belarus, Rasha da Ukraine sun amince da samar da hanyoyin kai agajin jin kai da kwashe fararen hula.

Mykhailo Podoliak, mashawarcin ofishin shugaban kasar Ukraine ne ya bayyana haka jiya, a shafin Twitter. Yana mai cewa an samu mafita game da samar da hanyoyin kai agajin jin kai.

A nasa bangaren, hadimin shugaban Rasha, kuma jagoran tawagar kasar a tattaunawar, Vladimir Medinsky ya ce, yayin zaman na jiya Alhamis, bangarorin biyu sun tattauna kan batutuwan da suka shafi ayyukan soji da na jin kai da warware rikicin dake tsakaninsu a siyasance.

Ya kara da cewa, sun fayyace matsayarsu a bayyane, kuma an yi kokarin cimma yarjejeniya game da wasu daga cikinsu. Yana mai cewa, samar da hanyoyin jin kai abu ne mai muhimmanci.

A jiyan ne kuma shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce matakan soji na musamman da ya dauka, na tafiya kamar yadda aka tsara. Ya bayyanawa mambobin dindindin na majalisar tsaron kasarsa cewa, an aiwatar da dukkan ayyukan da aka tsara cikin nasara. (Fa’iza Mustapha)