logo

HAUSA

Kasar Sin na daya daga cikin wadanda suka taka rawar gani wajen yaki da annobar COVID-19

2022-03-04 14:03:10 CRI

Kakakin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin a zamanta karo na 5, Zhang Yesui, ya ce kasar Sin na daya daga cikin kasashen da suka fi taka rawa wajen yaki da annobar COVID-19.

Zhang Yesui, wanda ya bayyana hakan a yau Juma’a, ya ce burin Sin na kawar da cutar baki daya, ya dace da yanayin kasar. Kuma ita ce hanyar da ta dace, wadda ta samar da sakamako mai kyau. Ya kara da cewa, dukkan alkaluma, kamar na wadanda suka kamu da cutar da wadanda suka mutu da kuma na tattalin arziki, sun nuna cewa, kasar Sin daya ce daga cikin kasashen duniya da suka fi samun nasara wajen dakile annobar. (Fa’iza Mustapha)