logo

HAUSA

Wang Yi ya zanta da firaministan Iran

2022-03-03 14:42:29 CRI

A jiya Laraba ne babban dan majalissar gudanarwa, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya zanta da takwaransa na kasar Iran Hossein Amir Abdollahian ta wayar tarho.

Yayin tattaunawar, wadda ta gudana bisa gayyatar ministan harkokin wajen Iran, Hossein Amir Abdollahian ya ce har kullum, kasar sa na kara azama wajen ingiza ci gaban cikakkiyar hadin gwiwar dake tsakaninta da Sin, yana kuma fatan sassan biyu, za su kara fahimtar juna ta fuskar siyasada zurfafa aiwatar da tsare tsare, karkashin cikakkiyar hadin gwiwar su daga dukkanin fannoni.

Ministan ya ce Iran na goyon bayan aniyar kasar Sin, ta karbar bakuncin taro na 3, na ministocin wajen kasashe makwaftan kasar Afghanistan.

A nasa bangare kuwa, Wang Yi cewa ya yi, Sin a shirye take ta yi aiki tare da Iran, wajen bunkasa hadin gwiwa mai maana a sassa daban daban, da zurfafa cikakken hadin gwiwa, da nasarar manufofin da shugabannin kasashen biyu suka amince.

Ya ce kasar Sin za ta shirya taro na 3, na ministocin wajen kasashe makwaftan kasar Afghanistan a lokaci mafi dacewata yadda kasashen za su samu damar taka muhimmiyar rawa ga wanzar da ikon Afghanistan na jure dukkanin kalubale, a fannin wanzar da zaman lafiya da daidaito.   (Saminu)