logo

HAUSA

Babban jami’in NATO ya jaddada tasirin matakan diflomasiyya don warware rikicin Ukraine

2022-03-02 10:51:02 CRI

Sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg ya jaddada muhimmancin bin matakai na diflomasiyya don warware rikicin dake faruwa a halin yanzu a Ukraine.

Ya bukaci a gaggauta dakatar da yaki a Ukraine, sannan ya bukaci Rasha ta kwashe dakarunta, kuma a rungumi hanyoyin diflomasiyya don warware rikicin.

Ya ce, a yan makonnin da suka gabata, a martaninmu game da harin da Rasha ke kaiwa Ukraine, mun kara yawan tsaron da muke da shi ta sama, da ta kasa, da kuma ta ruwa.

Babban jamiin NATO ya ce, “a karon farko a tarihinmu, mun tura takarun tsaro na kungiyar NATO," jamiin ya bayyana NATO a matsayin kawance tsaro wanda ba ta da niyyar gwabza yaki da Rasha.

A jiya Talata, babban sakataren MDD, Antonio Guterres ya bukaci a samar da kudaden da za a yi amfani da su domin ayyukan jinkai ga masu neman agajin jin kai dake karuwa a Ukraine, da kuma kokarin kawo karshen rikicin.

Asusun wanda aka kaddamar a watanni uku don neman kudaden tallafawa Ukraine, inda ake neman dala biliyan 1.1 domin samar da muhimman tallafin jinkai ga mutane sama da miliyan 6 wadanda rikicin ya shafa da suka kauracewa gidajensu sakamakon hare-haren sojoji. Shirin agajin gaggawa na shiyyar yana bukatar dala miliyan 551 domin taimakawa yan kasar Ukraine wadanda suka tsere zuwa makwabtan kasashe, musamman kasashen Poland, da Hungary, da Romania da kuma kasar Moldova. (Ahmad Fagam)