logo

HAUSA

An kunna wutar gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ajin nakasassu a Birtaniya

2022-03-01 15:25:30 CRI

An kunna wutar gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta bana ajin nakasassu, wadda za’a gudanar a Beijing, a wani kauye mai suna Stoke Mandeville dake kasar Birtaniya.

Tun daga gobe Laraba, za’a hada wutar da aka kunna a Stoke Mandeville, da wutar da aka kunna a sauran wasu wurare 8, don ta zama wutar gasar Olympics ta lokacin sanyi ta bana ajin nakasassu ta Beijing, inda za’a fara mika wutar yola har zuwa ranar 4 ga wata, ranar da za’a kaddamar da gasar.

Shugaban kwamintin shirya gasar wasannin Olympics ajin nakasassu na kasa da kasa, Mista Andrew Parsons ya bayyana fatan alheri game da hakan ta kafar bidiyo. (Murtala Zhang)