logo

HAUSA

Kwararru a nahiyar Afirka sun yi kira da a samar da kudaden aiwatar da matakan dakile sauyin yanayi tun daga tushe

2022-03-01 11:20:29 CRI

Kwararru a nahiyar Afirka sun bayyana bukatar samar da isassun kudaden gudanar da ayyukan dakile tasirin sauyin yanayi tun daga tushe, domin baiwa nahiyar damar jurewa alamun sauyin yanayi kamar fari, da karuwar zafi, da wutar daji, tare da yaduwar cututtukar da wasu halittu ke bazawa.

Kwararrun sun yi wannan kira ne a jiya Litinin a birnin Nairobin kasar Kenya, yayin taron kaddamar da rahoto na 6 na sassan gwamnatocin nahiyar game da sauyin yanayi ko IPCC a takaice, taron da ya gudana a gefen ci gaban taron dandali na 5, na hukumar MDD mai lura da muhalli ko UNEA-5. 

Kwararrun dai na ganin cimma nasarar kafa tsarin da zai baiwa nahiyar Afirka damar jure mummunan tasirin sauyin yanayi, da muhalli mai inganci, ya dogara ne ga nasarar samar da isassun kudaden gudanar da muhimman ayyuka masu nasaba da hakan.  (Saminu)