logo

HAUSA

Sin ta yi maraba da shawarwarin Ukraine da Rasha

2022-03-01 19:18:12 CRI

              

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Talata cewa, kasarsa tana goyon bayan duk wani yunkuri na diflomasiyya da zai taimaka wajen warware rikicin kasar Ukraine cikin lumana, kana tana maraba da kaddamar da shawarwarin zaman lafiya tsakanin kasashen Rasha da Ukraine.

Wang Wenbin ya bayyana haka ne a yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa, a matsayin martani ga shawarwarin da tawagogin kasashen Rasha da Ukraine suka gudanar a yankin Gomel na kasar Belarus jiya Litinin.

Wang ya kara da cewa, kasar Sin na fatan bangarorin biyu za su ci gaba da yin shawarwari da neman hanyar siyasa wajen warware matsalolin tsaro na bangarorin biyu, da tabbatar da tsaron bai daya a nahiyar Turai, da kuma samar da dauwamamman zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar Turai. (Ibrahim)