logo

HAUSA

An Kaddamar Da Dandalin Hidima Na Musamman Na Duniya Na CMG

2022-02-28 19:24:14 CRI


Litinin din nan ne, aka kaddamar da dandalin hidimar kafofin watsa labarai mai suna All Media Service Platform (AMSP) wanda babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG da abokan huldarsa na kafofin watsa labaru na duniya suka kirkiro a hukumance.

Shen Haixiong, shugaba kuma babban editan CMG ne ya sanar da kaddamar da dandalin a wani biki, da ya samu halartar shugabannin kafofin yada labarai da kungiyoyi kusan 30 daga sassan duniya.

Shen ya ce, alkaluman kididdiga sun nuna cewa, jimillar mutane biliyan 62.814 ne suka kalli rahotanni da aka watsa labarai game da gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ta shekarar 2022, ta dandalin CMG, wanda ya zarce na gasar wasannin Olympics ta lokacin zafi ta Tokyo ta shekarar 2020. Haka kuma kimanin gidajen talabijin 2,107 da sabbin kafafen yada labaransu a kasashe da yankuna 110 na duniya, sun ba da misali tare da yada shirye-shirye da CMG ya tsara har sau 97,000. Wannan sabon ci gaba na hadin gwiwar kafofin watsa labarai da ayyuka na musamman ne suka kai ga kaddamar da wannan dandali.

Shen ya kuma jaddada cewa, ta hanyar gina wannan dandali, CMG na fatan fadada sabbin tashoshi na hadin gwiwar kafofin watsa labaru na duniya, da kara tabbatar da ka'idar kare gaskiya komai dacinta, da tinkarar kalubale da samun nasara tare, da kuma karfafa kyawawan dabi'un bil Adama. (Ibrahim)