Yau Laraba 26 ga wata, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Yu Zhengsheng ya gana da shugaban kwamitin kula da harkokin tattalin arziki da al'umma na kasar Kongo Brazzaville Jean-Marie Tassoua a nan birnin Beijing.
Yayin ganawar, Yu Zhengsheng ya nuna cewa, a shekarun baya, kasashen biyu sun samu saurin bunkasuwar dangantakar dake tsakaninsu. Sin na fatan hadin kai da kasashen Afrika ciki hadda Kongo Brazzaville, domin yin amfani da zarafi mai kyau wajen habaka hadin gwiwa a tsakaninsu, da kara zurfafa zumuncin dake tsakaninsu. Ban da haka, kasar Sin na fatan kasashen biyu za su kara tuntubar juna ta fuskar tattalin arziki da al'umma ta hanyoyi daban-daban a dukkan fannoni, a kokarin sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar sada zumunci a tsakaninsu.
A na shi bangaren, Jean-Marie Tassoua ya ce, kwamitinsa zai ta hada kai da kasar Sin domin ba da gudummawa wajen zurfafa dangantakar dake tsakaninsu. (Amina)




