A madadin babban sakataren MDD Ban Ki-Moon, kakakinsa ya bayar da sanarwa a ranar 5 ga wata, inda ya nuna rashin jin dadi kan batun fashewar bama-bamai a dakin ajiyar makamai a ranar 4 ga wata a garin Brazzaville, babban birnin kasar Congo.
A cikin sanarwar, Ban Ki-Moon ya bayyana cewa, a yayin da ake fama da wannan wahala, MDD za ta ci gaba da ba da taimakon jin kai da gudanar da aikin ceto.
Bisa labarin da aka bayar, batun fashewar bama-bamai a dakin ajijar makamai da ta abuku a garin Brazzaville, babban birnin kasar Congo,fashewar bama-baman ta yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 146, a yayin da wasu fiye da dubu daya suka ji rauni, daga cikin mamatan, akwai ma'aikata Sinawa guda 6.(Lami)




