Shugaban Kongo (Brazzaville) Sassou Nguesso da manyan jami'an gwamnatin kasar da jakadun kasashen waje dake kasar sun halarci bikin jana'izar, kuma sun ajiye furanni a gaban kesheyinsu don nuna girmamawa ga wadanda suka kwanta dama. Shugaban kasar Sassou Nguesso ya gana da wakilan kamfanin Beijing Construction Engineering Group (BCEG) don isar da alhini ga jama'ar kasar Sin baki daya.
Ministan harkokin kwadago da jin dadin jama'a Florent Tsiba ya yi jawabi a wurin, inda ya jajanta game da mutuwar ma'aikatan kasar Sin guda 6 a hadarin, kuma ya gode wa ma'aikatan kasar Sin don kokarin da suka yi wajen bunkasuwar Kongo (Brazzaville).
A ran 4 ga wata a birnin Brazzaville, babban birnin kasar Kongo Brazzaville, an samu wata fashewa a wani dakin ajiye makamai, lamarin da ya janyo mutuwar mutane matuka. Fashewar ta lalata wurin da ma'aikatan kamfanin Beijing Construction Engineering Group ke zaune, ma'aikata 6 daga kasar Sin sun mutu a sakamakon hadarin, yayin da goma sha suka ji rauni. (Hauwa)




