
Sama da mutane 1500 ne suka samu rauni a cikin wannan lamari kamar yadda alkaluma daga bangaren asibitocin Brazzaville suka tabbatar. Emilienne Raoul, ministan kula da harkokin al'ummar da lamuran jin kai da agaji na kasar ya sanar da manema labarai cewa, gwamnatin ta girka wani sansanin da zai dauki mutane 5000 da suka kasance ba su da muhalli, suna kuma bukatar kayayyakin masarufi da magungunan kariya daga cutar zazzabin malariya, zawo da mura.
Emilienne Raoul ya kuma yi kira zuwa ga al'umma da ta kawo taimako ga wadanda ba su da muhalli.
Kafin wannan kuma, bisa adadin da dakunan ajiyar gawawwakin da ke Brazzaville ya sanar, an ce, a kalla mutane 215 ne suka rasa rayukansu a sakamakon tarwatsewar bama-baman.(Abdou Halilou)




