in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana jiran sakamakon shari'ar da aka gudanar kan wasu maharba guda 2 a kasar Kongo Brazaville
2011-12-08 15:18:13 cri
A ranar 13 ga watan Disamba ne, ake sa ran samun sakamakon hukumcin da kotun garin Owando ta yanke, a kan masu farautar nan guda 2 da aka kama da haurunan giwa.

Tun dai ranar 29 ga watan Oktoban da ya gabata ne, 'yan sanda tare da jami'an kula da fasalin aiwatar da dokar kare dabbobin daji, suka kama maharban a kusa da garin Makoua na kasar ta Kongo Brazaville. An dai gudanar da shari'ar ne tun ranar 17 ga watan Nubambar da ya gabata.

A lokacin da 'yan sanda suka kai samame a gidan maharban,sun tara da haurunan giwa guda 2, tare da wutsiyar giwa guda, da bindiga samfarin carabine 375. Maharban sun yi kokarin ba da hanci ga jami'in 'yan sandar na kudin sefa dubu 430, sai dai jami'in ya ki amincewa.

Dokar kasar Kongo bisa kan kare dabbobin daji ta haramta ajiye ko kasuwancin dabbobin daji kamar su giwa, baka, jan biri, damisa ko kuma wasu sassan jikinsu,bugu da kari dokar ta hana kasuwancin dabbobin da nau'insu ke shirin bacewa a kan doron kasa.

Sabo da haka , dukan wanda aka kama da hauren giwa, ana sa ran ya kashe ta ne, kamar yadda dokar ta yi amana. Dukan wanda aka kama da aikata wannan laifi zai yi zaman gidan yari na shekaru 5 da kuma biyan tara ta kudi miliyan 5 na sefa.(Abdou Halilou)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China