Bisa labarin da aka bayar, an ce, gwamnatin kasar za ta bada kudin taimako a kalla dala dubu 6 ga kowane iyali da wannan hadari yayi wa tasiri.
Ban da wannan kuma, ministan kula da tattalin arziki da manufofi da yankunan kasar Kongo Brazzaville Pierre Moussa ya sanar a ran 8 ga wata cewa, kasarsa za ta gina gidaje dubu 5 ga mutanen da gidajensu suka lalace a sakamakon hadarin.
Kana Moussa ya ce, ya zuwa yanzu, yawan 'yan gudun hijira na wannan bala'i a kasar ya kai 13854, kuma yawan mutanen da suka ji rauni da aka yi rajista a hukumomin likotoci na birnin Brazzaville ya kai 2315. Ban da wannan kuma, bisa labarin da kwamitin kula da aikin bada jinya bayan fashewar ya sanar cewa, ya zuwa ranar 8 ga wata, mutane kimanin dubu 1 suka sami sauki da barin asibitoci bayan da aka yi musu jinya.(Zainab)




