Ranar Lahadi 4 ga wata a Brazzaville babban birnin kasar Kongo Brazzaville, wasu abubuwa suka fashe a dakin ajiye makamai, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 206 yayin da dubban mutane suka raunana, daga cikinsu, akwai ma'aikata Sinawa 6 da suka mutu kamar yadda ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar ya tabbatar.
Wannan hadari ya faru ne a wannan rana da misali karfe 8, lamarin da ya yi sanadiyyar lalacewar gine-gine da dama, har ma da wasu motoci. Ban da wannan kuma, lamarin ya katse harkokin sadarwa tare da haifar da cunkosa hanyoyi da kuma tsoratar da mutane.
Ministan tsaron kasar Kongo Brazzaville ya yi jawabi ta gidan telibijin bayan abkuwar hadarin, inda ya yi kira ga mutane da su kwantar da hankalinsu. Ya ce, wuta ce ta kama dakin ajiye makamai wanda ya haddasa fashewar dakin. Ya zuwa yanzu, ana kokarin kashe wutar domin dakatar da sake faruwar wata fashewar. A daren wannan rana, kakakin gwamnatin kasar ya ce, matsalar wutar lantarki ce ta haddasa hadarin da ya faru a safiyar wannan rana, ba hari ne da aka kai ba.(Amina)




